TAKE HAKKIN YAN JARIDA DA AIKI A NAJERIYA

Kalaman BULAMA KENAN

“KO INDA AKE YAKI KAMAR SU SYRIA, LIBYA, ETHIOPIA DA UKRAINE, YAN JARIDA SU NA AIKIN SU BALLE ZAMFARA”

RE:
RA’AYI NE DA KARIN HASKE KAN KALAMAN BULAMA MAI ZANE A JARIDA

HAND CORF

A najeriya, masu uwa a gindin murhu ne ke shanawwr su kamar ‘ya’yan gwal.

A tsarin dokar najeriya, kowa ne dan kasa nada yancin fadin albarkacin bakin sa tare da ikon shiga takarar kujerar wakilci da Kuma ikon a zabe sa.

Amman abun mamaki da Gwamnatin jihar zamfara ta dakatar da ayyukan gidajan yada labarai bisa ayyukan ta’addanci a jihar da sauran su, shin wai Yan jarida na daukar makami ne domin yakar Gwamnati ko amfani da kafafan su domin chachakar Gwamnati ba tare da hujja ba?

Shin ko hakan ne ya sanya Gwamnatin jihar zamfara ta gaza biwa shugaban Yan jarida da aka lakadawa dukan kawo huka ya sanya Gwamnatin jihar zamfara da ta tarayya ta gaza yin komai akai?

Allah yi kyauta da irin tauye hakkin Yan jarida a najeriya.

A baya ba da jimawa ba, Gwamnatin tarayya ta Samar da dokar yakar kalaman batanci da yada labaran kanzan kurege a najeriya, Wanda kafafan yada labarai suka bayar da goyan bayan su na tallafawa Gwamnati a yankar hakan, Amman yanzu wai kafafan yada labarai ne suka zamo abokan hamayyar Gwamnati.

Amman ba a Isa dai a Hana mu yancin fadin albarkacin bakin mu ba.

Ana wata ga wata dai a najeriya. 

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started