INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIUNA
Wallahi duniya ba komai bane, mutuwar Ka zata zo maka a lokacin da Baka yi tsammani ba, ka shirya ko baka shirya ba.
A yau juma’a ne na samu labarin rasuwar daya daga cikin dalibai na, wato Milcah Yashim Kognet, daliba Mai hazaka, ga hakuri da mutun ta na gaba da ita a makami tare da mutun ta na kasa da ita.
Labarin rayuwar ta a duniya ya tsaya, sai Saban rayuwa wato na kiyama.
Wallahi a zama na da Milcah, na san ta da kishin kasa da jajircewa wajan ganin ta cimma burin ta bisa baiwa Kowa hakkin sa ba tare da san zuciya ba.
A cikin watan daya gabata, ta Kira ni Kan mobilization na NYSC domin taje aikin bautar kasa bayan tsawan lokaci ba tare da Kaduna polytechnic ta tura ta ba, amsar dana bata shi ne, “kiyi hakuri, lokaci na nan tafe nan kusa”, ashe ba zata kara wata guda ba a rayuwar duniya ba.
Ke duniya wallahi abun tsoro ne, Allah Ka sa mu Gama da duniya lafiya, Ka sa mu rabu da iyayen mu lafiya, Allah Ka datar da mu hanya madai-daiciya ameen.

Leave a comment